Zulum ya jagoranci tawagar al’ummar Borno domin halartar sallar jana’izar Isa Gusau

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Lahadi, ya jagoranci tawagar al’ummar Borno domin halartar sallar jana’izar mai magana da yawunsa, Malam Isa Umar Gusau, wanda aka gudanar a babban masallacin kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Tawagar ta hada da Sanatoci masu wakiltar Borno ta tsakiya, Barista Kaka Shehu Lawan, Borno ta Arewa, Barista Mohammed Tahir Monguno, ‘yan majalisar wakilai daga Borno, sakataren gwamnatin jihar, Hon. Bukar Tijjani da kuma babban jami’in kamfanin na NNPC, Mele Kolo Kyari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *