Rundunar ‘yan sandan Kano ta bayyana shirinta na dakile duk wani hargitsin da ka iya tasowa biyo bayan hukuncin da kotu za ta yanke

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana shirinta na dakile duk wani hargitsin da ka iya tasowa biyo bayan hukuncin da kotun koli za ta yanke na gobe kan karar da gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar, NNPP, ya shigar kan korar da kotun daukaka kara ta yi masa.

Rundunar ‘yan sandan ta baiwa mazauna jihar tabbacin tsaron lafiyarsu kafin da kuma lokacin da kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Hussaini Gumel ne ya bayar da wannan tabbacin yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a ranar Alhamis.

Gumel ya bayyana cewa rundunar ta aiwatar da matakan tsaro domin baiwa mazauna jijar damar ci gaba da sana’o’insu na halal ba tare da wata barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.

Ya ce, “Mun tattara isassun jami’an tsaro da za su samar da tsaro a duk wuraren da ake tashe-tashen hankula, da suka hada da ofisoshin jam’iyyun siyasa, gidan gwamnatin jihar, hedikwatar INEC, bankuna da wuraren kasuwanci, masallatai, coci-coci, wuraren shakatawa da wuraren ajiye motoci kafin, lokacin da kuma bayan hukuncin.

“Ina ba da tabbacin kashi 100 cikin 100 ga duk mazauna jihar masu bin doka da oda da su gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” in ji Kwamishinan.

Ya ce jami’an tsaron da ke dauke da makamai za su kasance a duk wuraren da aka san su don tabbatar da cewa sun fara aikin sa ido da samar da tsaro a lokacin da kotun koli za ta yanke hukunci da kuma bayan yanke hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *