Mai magana da yawun gwamna Zulum, Isa Gusau ya rasu.

Mai taimakawa na musamman bangaren watsa labarai da tsare-tsare na Gwamna Babagana Zulum, Mallam Isa Gusau, ya rasu sakamakon rashin lafiya

Rahotanni da suka fito na cewa mai magana da yawun Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, Mallam Isa Gusau, ya rasu a wani asibiti da ke kasar Indiya.

A cewar rahotanni, Gusau shine mai magana da yawun Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasan Najeriya, a lokacin da ya ke gwamna a jihar Borno.

Kakakin gwamnan ya shafe kimanin wata guda a wani asibiti a Indiya yana jinyar wani ciyo da ba a bayyana ba kawo yanzu.

Rahoton ya kara da cewa Gusau ya easu ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, a wani asibitin kwararru a New Delhi, babban birnin Indiya, a cewar wata majiya da nemi a boye sunanta.

A cewar majiyar:

“Mun rasa Isa, ya suma na kimanin kwana uku, dukkanmu muna masa addu’ar samun sauki, amma abin bakin ciki ya rasu da yamma yau (jiya) a asibiti a New Delhi, Indiya.”

Source

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *