A yau ne kotun koli za ta yanke hukunci kan kararrakin da aka yi na gwamna a jihar Kano

A Kano, shari’ar tana tsakanin Gwamna Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP, da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC.

A yau Juma’a 12 ga Janairu 2023 ne Kotun Koli za ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan Jihar Kano, tsakanin Gwamna Abba Kabir Kano Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP da babban abokin hamayyansa, yi zama Nasir Yusuf Gawuna.

Kotun Koli za ta sanar da hukuncin ne bayan kawanaki 298 da zaben Gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris, 2023, wanda aka shafe sama da makonni 40 ana shari’a a kansa.

Shari’ar dai ta samu asali ne da karar da APC ta shigar gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano tana kalubalantar nasarar Gwamnan Abba, inda take neman a ayyana Gawuna a ma Abba.

Gwamna Abba da NNPP ne suka ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli a wannan shar’a mai cike da rudani ne domin ƙalubalantar ƙwace kujerarsa da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya ta yi.

Suna kuma kalubalantar yi da kuma shirinta na sauya rubutaccen hukuncinta — mai karo da juna — da ya tabbatar masa da kujerar.

Karo na biyu ke nan da gwamnan Kanon ke daukaka kara kan shari’ar, da nufin kare kujerarsa, da kuma rashin gamsuwa da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano  da  kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya  da suka kwace kujerarsa.

Shari’ar zaɓen dai ta shafe sama da kwanaki 300 tana ɗaukar hankalin jama’a, musamman ma bayan kundin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya kan shari’ar ya fito ɗauke da saɓanin hukuncin da aka karanta a zamanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *