‘Yan sanda sun kama karin mutum 3 da ake zargi da hannu harin jihar Filato.

An kama karin wasu mutum uku da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi a Jihar Filato.

Rundunar ’yan sanda ta ce mutane ukun na cikin wani gungun masu dauke da bindigogi da ya kai hare-hare a jajibirin Kirsimeti wadanda suka yi sanadin mutuwar akalla mutum 200.

A wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan kasar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Talata da maraice, ya ce mutanen na cikin mutum 67 da suka kama bisa zargin aikata laifuka daban-daban a fadin kasar.

“Mutanen da ake zargin su ne Ahmed Sulaimon da Balikisu Aliyu da Aboki Samuel. Bayan an kama su, an gano makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47 guda daya da kirar AK-49 guda daya da harsasai 1000 da kwanson harsasai biyar,” in ji Adejobi.

Ya kara da cewa “a halin da ake ciki mutanen suna tsare a hannun ‘yan sanda kuma suna taimakawa wurin bincike.

An ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga ne suka kaddamar da jerin hare-hare a kauyuka kusan ashirin a jihar ta Filato a jajibirin Kirsimeti.

Ana iya tuna cewa, hukumomi sun kama wasu mutum takwas mazauna yankin da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai.

Tun da fari, hukumomi sun ce mutum 163 ne suka mutu a hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos.

Sai dai yayin daMataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya kai ziyara a jihar ta Filato, shugaban karamar hukumar Bokkos Monday Kassah ya ce mutum 148 aka kashe a yankinsa.

Kazalika, an kashe mutum akalla 50 a kauyuka daban-daban na Karamar Hukumar Barkin Ladi, a cewar Dickson Chollom, wani dan majalisar dokokin jihar daga yankin.

“Muna rokonku da ku guji raba kawuna da kiyayya ga junanku, a yayin da muke kokarin ganin an yi adalci domin samar da zaman lafiya,” in ji Kashim Shettima a yayin da ya gana da jami’an gwamnati da sarakuna da kuma mazauna yankunan.

Olumuyiwa Adejobi ya kara da cewa “a yunkurin” rundunar ‘yan sanda na “kakkabe aikata laifuka a fadin kasar nan, sashen leken asiri da dabaru” ya yi nasarar kama mutum “67 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da sayar da makamai, da fashi da makami.”

“Kazalika ‘yan sanda sun kwace harsasai 5,454 da kwanson harsasai 300 da kananan bindigogi 68 da katin cirar kudi na ATM 33 da sauransu,” in ji kakakin ‘yan sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *