EFCC ta bada belin dakatacciyar ministar jin ƙai da yaƙi da talauci, Betta Edu.

Bayan shafe tsawon awanni tana shan tambayoyi, EFCC ta bada belin Betta Edu, dakatacciyar ministar jin ƙai da yaƙi da talauci.

Misis Edu ta mika kanta ga EFCC ranar Talata da safe kuma tun lokacin har zuwa dare tana hedkwatar hukumar kafin daga bisani a bada belinta

EFCC ta bada belin Edu ne bayan titsiye ta da tambayoyi na tsawon sa’o’i kan zargin ta bada umarnin tura kuɗi N585m zuwa asusun kai da kai na wani ma’aikaci.

A ranar Litinin ne Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya dakatar da Misis Edu daga ofis sannan ya umarci EFCC ta gudanar da bincike kan badakalar da ake zargin da hannunta.

Ba tare da ɓata lokaci ba hukumar EFCC ta aike da saƙon gayyata ga Edu, inda ta umarci ta kai kanta hedkwatar hukumar da ke Abuja ranar Talata.

Mun tattaro cewa Betta Edu ta amsa gayyatar da aka yi mata, ta kai kanta ofishin EFCC da safiyar Talata. Tun da ta isa hedkwatar EFCC, jami’an hukumar suka fara mata tambayoyi kan badaƙalar da ta auku a ma’aikatarta har zuwa dare lokacin da aka bada belinta.

Hukumar yaƙi da rashawa ta kwace fasfon tafiye-tafiya na Betta Edu kafin daga bisani su ba ta damar tafiya gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *