Tinubu ya dauki mataki don rage yawan kashe-kashen kudade da ake yi a gwamnati

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka inda yace wannan na daga cikin hikimar Tinubu don rage yawan kashe kudade da ake yi a gwamnati.

Ngelale ya ce matakin zai shafi ofishin shugaban kasa da mataimakinsa da kuma matar shugaban kasa.

Sauran ofisoshin sun hada da na ministoci da kuma shugabannin hukumomin kasar da sauransu.

Sanarwar ta ce shugaban ya kuma rage yawan mutane da za su rinka tafiya da shi da kuma mataimakinsa.

An kayyade yawan wadanda za su kasance da matar shugaban kasa yayin tafiye-tafiye a gida da waje. Sanarwar ta ce:

“Tinubu ya bukaci dukkan tafiye-tafiyen a rage su, wannan umarni ne ba shawara ba, mataimakin shugaban kasa da ma’aikatansa duk ya shafe su.

Ajuri Ngelale

“Wannan umarni ya zai datse yawan kashe kudaden da kaso 60.”

Ajuri Ngelale

Tafiye-tafiyen kasashen waje: – Shugaban kasa – mutane 20

Mataimakinsa – mutane 5

Matar shugaban kasa – 5

Tafiye-tafiyen cikin gida:

Shugaban kasa – mutane 25

– Mataimakinsa – mutane 15

– Matar shugaban kasa – mutane 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *