Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar harkokin jin kai da yaye talauci, Betta Edu.

Shugaba Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da ministar harkokin jin kai da yaki da talauci, Dokta Betta Edu daga aiki ba tare da bata lokaci ba.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana dakatar da ministar a wata sanarwa da aka wallafa a shafin fadar shugaban ƙasa na X ranar Litinin.

Idan za a iya tunawa,Tinubu ya bayar da umarnin yin bincike a Ma’aikatar Jinkai kan zargin badakalar N585m.

Wannan dai yazo daidai lokacin da ‘yan Najeriya suke ce-ce-kuce bayan wasu takardu sun nuna cewa Ministar Jinkai Betta Edu ta bayar da umarni ga Akanta Janar ta kasar ta tura N585m ga asusun wata mata mai suna Onlyelu Bridget Mojso a matsayin tallafi.

Sai dai Akanta Janar ta Nijeriya Dakta Oluwatoyin Madein ta ce ofishinta ba ya biyan kudi a madadin ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan ayyukan da suke aiwatarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *