Kotu ta ci tarar gwamnati tarayya da EFCC, naira miliyan 100 kan tauye hakkin Emefiele

Alkalin Babbar kotun birnin tarayya Abuja  ya hana Gwamnatin Tarayya da jami’anta sake kama Emefiele ko tsare shi ba tare da umarnin kotu ba.

Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bayyana tsawaita tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emfiele, ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba a matsayin tauye hakkinsa.

Kotun ta kuma ci tarar zunzurutun kudi Naira miliyan 100 ga gwamnatin tarayya da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Ta kuma hana Gwamnatin Tarayya da jami’anta sake kama Emefiele ko tsare shi ba tare da umarnin kotu ba.

Kotun ta yanke hukuncin ne a cikin wata babbar kara ta kare hakkin dan adam da tsohon gwamnan CBN ya shigar biyo bayan tsawaita tsarewar da aka yi masa a hannun Hukumar DSS.

Ya roki kotun da ta umarci wadanda ake kara da su biya shi diyyar tsabar Kudi Naira biliyan 1 tare da hana su ci gaba da kama shi ko kuma a tsare shi.

Rahma ta rawaito cewa an kama tsohon shugaban na CBN ne a ranar 10 ga watan Yuni jim kadan bayan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi masa.

Wadanda ake tuhuma a cikin karar sun hada da Gwamnatin Tarayya, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya; EFCC da shugabanta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *