Mata da miji sun shiga hannun hukuma kan zargin kashe mutumn a kasuwar Ogun

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta damke wannan mata da miji ne bayan mutuwar abokin fadan nasu mai suna Mista Mark Kalu.

A safiyar Lahadi ne kakakin rundunar, SP Omolola Odutola, ta sanar a Abeokuta cewa Mista Kalu wanda ya samu raunuka a sassan jikinsa a yayin fada da ma’auratan ya mutu.

SP Odutola ta ce, “Rikicin Mista Kalu da ma’auratan a kasuwa ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

“Babaloja na Osiele da kuma shugabannin kabilar Igbo sun yi kokarin ganin an sasanta lamarin cikin ruwan sanyi.

“Amma dai yanzu wadanda ake zargin suna hannun ’yan sanda ana gudanar da bincike.”

Ta ce gawar mamacin kuma an kai ta Babbar Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Idi Aba, Abeokuta domin gudanar da bincike.

Mata da mijin da ake zargin dai sun ba hamata iska da  Mista Kalu ne a ranar 8 ga watan Oktoba 2023, a Kasuwar Osiele da ke Jihar Ogun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *