Jami’ar ATBU ta karyata batun aiki da malaman bogi

Hukumar gudanarwar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta bayyana wani bincike a matsayin labarin karya da tatsuniyoyi kawai da Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) ta bayyana cewa ta bankado malaman bogi kusan 100 a wasu jami’o’in Najeriya har da ita a ciki.

A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Zailani Bappah ya raba wa manema labarai a jiya, ya ce:

“Labarin na tatsuniyar almara ce kawai, wani shiri ne na kirkire-kirkire kuma wani yunkuri ne na bata sunan jami’ar a idon Duniya”.

Zailani Bappah

A cewar sanarwar, labarin ya nuna cewa a cikin 100 da ake zargin malaman jami’ar akwai sunayen mutane bakwai a matsayin ma’aikatan jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

ATBU ta ce babu daya daga cikin malaman da aka ambata ma’aikacin jami’ar, kuma bai yi mu’amala da jami’ar a kowane lokaci ba a kowane irin matsayi.

Saboda haka Zailani Bappah yayi kira ga yan Nijeriya dama sauran mutane dake alaka da Jami’ar da su gaggauta watsar da abinda ya kira maganganun karya da ake yadawa akan Jami’ar.

Inda ya tabbatar da cewar wadannan alkaluma da hukumar Jami’o’i ta NUC ta fitar babu kamshin gaskiya a cikinsu illa son rai da tsantsar kuskure duba da cewar babu daya daga cikin Farfesoshin da ke cikin jadawalin da ya taba aiki da Abubakar Tafawa Balewa University

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *