An Sako Oscar Pistorius Daga Gidan Yari Shekaru 11 Bayan Ya Kashe Budurwarsa

An saki Oscar Pistorious dan wasan tsere na gasar Olympics daga gidan yari a kasar Afirka ta Kudu bayan shekaru 11 a gidan yari bisa laifin kashe budurwar sa.

An sallami Oscar Pistorius, dan tseren nakasassu da ya rasa kafafunsa biyu, ne a safiyar Juma’ar da ta gabata. Ya harbe budurwarsa, Reeva Steenkamp, sama da shekaru goma da suka wuce, kuma hukumar ta Afrika ta Kudu ta yanke shawarar sake shi a watan Nuwambar 2023.

Hakan ya faru ne saboda ya shafe rabin hukuncin daurin shekaru 13 da aka yanke masa, wanda dokar Afirka ta Kudu ta tanada.

An saki Oscar Pistorius daga kurkukun da ke kusa da Pretoria a ranar Juma’ar da ta gabata, amma kuma dole ne ya bi wasu ka’idoji har sai lokacin da aka yanke masa hukunci a shekarar 2029.

Mahaifiyar Reeva Steenkamp, ta bayyana cewa burinta a yanzu shi ne ta zauna lafiya bayan an sako Pistorius. ta na cewa “baza a taba samar da wani adalci ba in har masoyanka da ka rasa baza su taba iya dawo wa a raye ba”.

Pistorius ya harbe Reeva a shekara ta 2013, yana mai cewa ya yi mata kutse ne, ba wai a zazzafar muhawara ba kamar yadda masu gabatar da kara suka nuna.

A yayin shari’ar da ta dauki hankalin duniya, Pistorius ya ce bai aikata kisan kai ba kuma ya musanta tuhumar da ake yi masa na mallakar bindiga da ke da alaka da mutuwar Steenkamp. Da farko, an yanke masa hukuncin shekaru biyar a kan laifin kisa a shekara ta 2014. Amma, wata babbar kotu ta canja shi zuwa kisa bayan shekara guda, wanda hakan ya ƙara masa zaman gidan yari zuwa shekaru shida.

Masu gabatar da kara sun daukaka kara, inda suka ce hukuncin ya yi sassauci. A shekara ta 2017, Kotun Kolin daukaka kara ta Afirka ta Kudu ta yanke wa Pistorius hukuncin daurin shekaru 13 da watanni biyar.

A cikin Maris 2023, Pistorius ya cancanci yin afuwa, biyo bayan wata doka ga fursunonin da suka cika rabin hukuncin da aka yanke musu kuma suka cika sharuɗɗa kamar kyawawan halaye. Wannan wani bangare ne na “Adalcin Maidowa” na ƙasar, wanda ke baiwa masu laifi damar amincewa da ɗaukar alhakin ayyukansu.

Ma’aikatar Kula da Gyaran Jama’a (DCS) ta bayyana cewa Pistorius zai kammala sauran hukuncin da aka yanke masa a tsarin gyaran al’umma.

Dole ne ya halarci shirye-shirye kan cin zarafi na jinsi kuma ya ci gaba da kula da halayensa da kokarin gyara su musamman fushi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *