Kamfani Amurka ya ba Gwamnatin Najeriya tallafin jiragen ruwa marasa matuka 2

Kamfanin Swiftship na kera makamai ga sojojin Amurka ya ba gwamnatin Najeriya tallafin jiragen ruwa marasa matuki guda biyu, Jiragen sun hada da S2 da S3 Swift Sea Stalkers.

Kamfanin ya bayar da gudummawar ne yayin ziyarar da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya kai a kwanakin baya.

A cewar wata sanarwa a ranar Juma’a ta bakin Daraktan yada labarai na ma’aikatar, Henshaw Ogubike, ministan ya tafi Amurka ne domin duba cibiyoyin manyan kamfanonin da ke samar da kayan aikin soja a kasar.

Da yake gabatar da jiragen da ba a bayyana sunayensu ba ga shugaban kasa Bola Tinubu, ministan ya bayyana cewa, jiragen za su taimaka wajen kare tekun kasar nan da ma sauran yankuna.

Ya bayyana cewa za a kai kayan aikin ne zuwa yankin Neja Delta, yankin tafkin Chadi, da sauran yankunan ruwa na kasar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ministan tsaro ya mika wa shugaban kasa Bola Tinubu jiragen ruwa marasa matuki guda biyu a fadar Villa domin su taimaka wajen yaki da rashin tsaro a magudanan ruwan mu musamman da ma kasa baki daya.

Kamfanonin jiragen ruwa na Swift Ship da ke Amurka ne suka bayar da tallafin jiragen ruwa guda biyu marasa matuki ga gwamnatin Najeriya.

“Da yake gabatar da nau’ukan jiragen guda biyu, S2 da S3 Swift Sea Stalkers, ya ce jiragen na zamani ne wanda wata sabuwar fasaha ce da za a yi amfani da ita wajen yaki da rashin tsaro a yankin Neja-Delta, yankin tafkin Chadi, da sauran yankunan ruwa na kasar.

“Za a iya tunawa cewa kwanan nan Ministan ya kai ziyarar aiki Amurka kuma ya duba NEANY, Swift Ships, da OCR Global, wani kamfani na haɗa kayan aikin soja a Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *