Mazaunin Abuja suna cigaba da nuna damuwarsu kan yawaitar garkuwa da mutane a yankin babban birnin tarayyar.

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da masu garkuwa da mutane da ke addabar babban birnin tarayya Abuja, musamman yankunan Bwari da Dei Dei, sun yi garkuwa da sama da 96 a cikin kwanaki 21.

Mazauna karamar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya da kuma al’ummar yankin na cikin fargaba a halin yanzu saboda hari ‘yan bindiga suke kai musu.

Hare-haren na baya bayan nan sun faru ne a ranar 1 ga watan Junairu, 2024 da misalin karfe 11:30 na rana, inda aka yi garkuwa da wani babban jami’in Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja, AEDC, da wasu ‘yan uwa da suka hada da matarsa ​​da wani yaro. Makonni uku da suka gabata, a ranar Asabar, 9 ga watan Disamba, 2023, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 23 a yankin Dei-Dei da ke karkashin karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya.

An kwashe mutanen ne daga gidajensu tsakanin misalin karfe 8 na dare zuwa karfe 9 na rana. Mai Unguwar Dei-Dei, Ibrahim Galadima, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya ce bayan kimanin sa’a guda ne jami’an tsaron yankin suka kubutar da 7 daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su a cikin daji.

Ya zuwa ranar 24 ga Disamba, 2023, an ce an sace mutane 25 a Bwari, inda uku suka rasa rayukansu a hare-haren.

A ranar Asabar, 23 ga Disamba, 2023, ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Garam da ke kan hanyar Bwari na tsawon mintuna biyar. A yayin wannan farmakin sace wani Fasto mai alaka da Redeemed Christian Church of God (RCCG) tare da yin garkuwa da mutane 13.

A ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, ‘yan bindigar sun sake kai farmaki a yankin Kuduru da ke kan iyaka da Garam, inda suka yi awon gaba da mutane 18.

Har ila yau, a ranar Juma’a, 29 ga watan Disamba, maharan sun kai hari Ahzu, inda suka kashe mutane uku tare da yin awon gaba da wasu takwas.

Wata mazauniyar Garam, Misis Juliana, ta ba da labarin yadda ‘yan bindiga suka fara shiga wani gida da ba daidai ba inda suka kama wasu maza biyu.

“Lokacin da suka isa wurin, sai suka yi garkuwa da dangin baki daya, amma yayin da suke barin gidan, sai suka harbe mutumin, wanda Fasto ne a Cocin Redeemed Christian Church of God a gaban matarsa ​​da ‘ya’yansu uku.”

Miss Juliana

Mazauna yankin sun ce maharan sun fito ne daga jihar Kaduna. Danladi Iyah shugaban karamar hukumar Tafa a jihar Neja ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce:

“A Garam, an yi garkuwa da mutane tara, yayin da aka harbe mutum daya, sannan kuma a Kuduru, an sace mutane bakwai amma ba a rasa rai a wurin ba.”

Danladi Iyah

Wata majiya, wadda ba ta so a ambaci sunan ta saboda dalilan tsaro, ta ce a harin da aka kai a Ahzu, wanda ya faru a ranar 28 ga watan Disamba, an harbe biyu har lahira, uku kuma suka jikkata. “Lokacin da aka yi irin wannan aikin, su (‘yan fashi) kan dauki duk wanda suka gani.

“Suna kawo mana hari da misalin karfe 11 na dare zuwa karfe 11:30 na dare. Harin da aka kai wa al’ummar Garam ya faru ne kwana guda gabanin Kirsimeti, wato ranar 24 ga wata.

“’Yan bindigar sun kai hari Kuduru kwanaki uku da suka wuce, yayin da aka kai wa Ahzu hari jiya da daddare da misalin karfe 11:30 na dare, lokacin da suka saba kai hari.

“Mun zagaya yau (jiya) tare da dukkan kayan tsaro don ganin yadda za mu iya shawo kan lamarin, wata kila don gujewa sake aukuwar irin wannan lamari.

Har ila yau, mazauna garin na zargin hadin baki tsakanin ‘yan fashi da jami’an tsaro.

A cewarsu, sojojin da aka tura yankin na da nisa daga inda ‘yan bindigar suka kai hari a ranar 1 ga watan Janairu.

Har zuwa lokacin da ake wannan rahoto, tuni mazauna yankin na shirin gudanar da zanga-zangar lumana, amma har yanzu shugabannin al’ummomin sun yi ta kiraye-kirayen su kwantar da hankula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *