Kotu ta baiwa gwamnatin Kano wa’adin kwanaki 7 don amsa korafin kananan hukumomi 44

A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta baiwa gwamnatin jihar Kano wa’adin kwanaki bakwai kan karar da kananan hukumomi suka shigar

Kotun ta ba da wa’adin ne don gwamnatin jihar ta yi martani kan zarge-zargen da ake yi a kanta.

Mai shari’a Donatus Okorowo ne ya bayar da wannan umarni, a wani hukunci, jim kadan bayan lauyoyin ko wane bangare sun gabatar da bahasi kan shari’ar da ake yi.

A ranar Alhamis 28 ga watan Disamba, Okorowo ya dakatar da bukatar da ke neman hana Gwamna Abba Kabir taba kudaden kananan hukumomin.

A madadin haka, ya umarci wadanda ake karar su gurfana a gaban kotun a ranar 3 ga watan Janairu. Ya bukaci gurfanar ta su ce don ba da dalili kan meyasa ba za a tabbatar da bukatar masu karar ba.

A makon da ya gabata kotun ta dakatar da hana gwamnan kan amfani ko kuma gudanar da kudaden asusun kananan hukumomin.

Sai dai gwamnatin jihar ba ta ce komai ba game da hukuncin kotun da ta gabatar a makon da ya gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *