Hukumar Hisbah za ta fara kamen masu bara a Katsina

Hukumar Hisbah za ta far kamen masu bara a fadin kananan hukumomi 34 da ke Jihar Katsina.

Babban Kwamandan Hisbah na jihar, Dokta Aminu Usman (Abu-Ammar), ya ce hukumar za ta kori duk mabarata da ba ’yan asalin jihar ba ne zuwa jihohinsu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana jaddada aniyar hukumar Hisbah ta kawar da mabarata daga titunan jihar.

Dokta Aminu Usman ya ce, “gwamantin Katsina na yin duk mai yiwuwa don kawar da bara a titunan jihar, saboda bara ba ta daga cikin addinmu, sai dai ma zubar da kimar addininmu da al’ummarmu da take yi.

“Dokar da ta kafa hukumar Hisbah ta ba mu ikon bin lungu da sako mu tantance mabarata, mu gano mabukata na ainihi a cikinsu, mu mika su ga Hukumar Zakka da Wakafi domin ta tallafa musu,” in ji shi.

Shugaban na Hisbah ya ce gwamnatin jihar ta kafa hukumar Zakka da Wakafi ne musamman domin tallafa wa mabukata.

Abu-Ammar ya ce wadanda ba ’yan asalin Jihar Katsina ba ne daga cikin wadanda aka gano kuma za a mayar da su johohinsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *