An kai sabon hari a filato

Jami’an tsaro sun tabbatar da mutuwar mutane a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai a Karamar Jos ta Gabas a Jihar Filato.

A daren Asabar ne ’yan bindiga suka kai harin, inda suka kashe wani mahaifi da dansa a yankin Durbi da ke karamar hukumar.

Shaidu sun ce mutanen unguwar sun yi fito-na-fito da maharan, kuma sun yi nasarar kashe daya daga cikin ’yan bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *