Majalisar Dattawa ta bukaci shugabannin tsaro kan harin filato

Majalisar Dattawa ta bukaci shugabannin hukumomin tsaro su bayyana a gabanta su tambayoyi kan kisan gilla da aka yi wa mutane 145 da Kirsimeti a Jihar Filato.

’Yan bindiga sun yi wannan aika-aika ne kauyuka 23 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi inda suka jikkata daruruwan mutane suka lalata dukiyoyi daga ranar Asabar har zuwa safiyar Litinin, Kirsimeti.

Majalisar ta ce hare-haren da ’yan bindiga suka kai a tare a lokaci guda ya nuna akwai gazawa wajen samun bayanan sirri na tsaro.

Bayan kudirin da Sanata Diket Plang daga jihar ya gabatar a zaman majalisar na ranar Asabar, ta gayyaci daukacin shugabannin hukumomin tsaro su zo su yi bayani kan kashe-kashen a safiyar Litinin domin bai wa majalisar damar daukar mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *