Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin gadar Dan Agundi

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin Gadar Dan Agundi a kan kudi naira biliyan 15.9 da kuma Gadar Tal’udu a kan naira biliyan 14.45

Wannan aikin ne yana bisa tsarin hadaka tsakanin kananan hukumomi da matakan gwamnatin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ayyukan 2 za su kawo bunkasar arziki a jihar Kano da kuma rage cinkoson ababen hawa a yankunan da aka sa gadoji.

Gwamnan ya kaddamar da aikin ne bayan wata Kotun Tarayya ta hana kafa doka hana gwamnatin jihar Kano amfani da kudin kananan hukumomi a aikin.

Kotun da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin wucin gadin ne bayan shugabannin kananan hukumomin jihar 44 sun yi karar gwamnatin jihar suna neman a hana ta amfani da kudadensu a aikin.

Rahma ta gano cewa a ranar Alhamis ne kotun ta ba da umarnin, Juama’a kuma Gwaman Abba ya kaddamar da aikin wanda aka ba wa kamfanin CGC Nigeria Limited.

Kawo yanzu dai gwamnatin bata magantu ba game da umarnin da kotu ta bayar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *