Rundunar sojin Najeriya ta yi wa sabbin manyan hafsoshi 47 ado da manyan mukamai na Manjo Janar

A yau Alhamis ne rundunar sojin Najeriya ta yi wa wasu sabbin manyan hafsoshi 47 ado da manyan mukamai na Manjo Janar.

Rundunar ta bukace su da su kara kaimi wajen tunkarar kalubalen tsaro a kasar nan.

Majalisar sojin kasar, a ranar 21 ga watan Disamba, ta amince da karin girma ga birgediya janar 47 zuwa mukamin Manjo Janar.

Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce karin girma da aka yiwa jami’an, shaida ce ta tsawon shekaru da suka kwashe suna aiki tukuru da sadaukarwa wajen yi wa kasa hidima.

A cewarsa, ya bukaci jajircewa, da’a, da juriya kafin daga bisani su tashi daga mukaminsu, inda ya kara da cewa, dukkansu sun nuna kwarewa ta musamman na shugabanci, da tunani mai zurfi da kuma zurfin fahimta a yayin gudanar da ayyukansu.

“Gudunmawar da kuka bayar ga rundunar sojin Najeriya na da matukar kima, kuma muna da tabbacin za ku ci gaba da yi wa al’ummarmu hidima da daraja.

“Yayin da muka murnar ci gaban ku, ina roƙon ku da ku ci gaba da jagoranci ta hanyar misali da zaburar da wasu don inganta sawun ku,” in ji shi.

Bello Matawalle

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *