Gwamnan Ondo, Rotimi Akerodolu ya rasu

Gwamna Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya rasu bayan ya sha fama da jinya. 

Wata majiya daga iyalinsa ta shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa Akeredolu ya rasu a Legas.

Rahma ta samu labarin cewa likitocin gidan gwamnati ne suke kula da shi har lokacin da ya rasu.

“Akeredolu ya rasu; Ya rasu a Legas,” in ji majiyar.

Yana da shekaru 67 a duniya.

Gwamnan da ke fama da rashin lafiya ya dawo Najeriya ne a watan Satumba bayan hutun jinya na watanni uku a Jamus.

Ya dawo ofishinsa bayan da shugaba Bola Tinubu ya umarce shi da ya mika mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *