An rantsar da Lucky Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar Ondo

An rantsar da mataimakin gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar bayan rasuwar gwamna Oluwarotimi Akeredolu.

Babban alkalin jihar Ondo, Justice Olusegun Odusola, ne ya rantsar da Aiyedatiwa a matsayin gwamnan farar hula na bakwai a jihar.

A ranar Laraba 27 ga watan Disamba 2023 Gwamna Akeredolu ya mutu a kasar Jamus sakamakon cutar sankarar bargo da ta kama shi.

An rantsar da Aiyedatiwa a ofishin gwamna da ke Akure ranar laraba da misalin karfe 4:15 na yamma.

Wadanda suka halarci bikin rantsuwar sun hada da shugaban majalisar dokokin jihar, Olamide Oladiji, sakataren gwamnatin jihar, Gimbiya Oladunni Odu da shugaban jam’iyyar APC mai mulki a jihar, Ade Adetimehin.

Sauran sun hada da ‘yan majalisar zartarwa, masu rike da mukaman siyasa, da sauran ‘yan jam’iyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *