Sadiya Umar Faruk: banida masaniya akan abinda ake zargina da aikatawa

Tsohuwar ministar harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban jama’a lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, Sadiya Umar-Farouq ta bayyana cewa bata san wani dan kwangila mai suna James Okwete ba wanda rahotanni da dama da ke alakata ta da shi.

A wani sako da ta wallafa a shafin ta na X(twitter) ta ce:

“Na yi wa al’ummar kasar Najeriya hidima da kowane irin nauyi, kuma a shirye ta ke ta kare matakin da ta dauka a duk lokacin da aka bukaci hakan”

Sadiya Umar Faruk

Haka ta biyo bayana rahotanni da suka bayyana cewa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC ta kama Okwete bisa zargin karkatar da Naira Biliyan N37.

Ta kara da cewa:

“James Okwete bai yi aiki daniba kuma bai wakilce ni ta kowace hanya ba,saboda haka a shirye nake da in amsa kowace irin tambaya da za a min”

Sadiya Umar Faruk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *