FRSC: “Mutum 4 sun mutu, 59 sun jikata a hatsari da ya afku a hanyar Kaduna-Abuja”

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa, FRSC ta tabbatar da mutuwar mutum 4, sannan wasu 59 sun samu rauni sakamakon hatsarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kabir Nadabo, Kwamandan hukumar a jihar, ya ce hatsarin ya ritsa ne da wata tirela mai lamba MKA 99YS a kauyen Sabon Sara da misalin karfe 03:30 na safiyar Talata.

Kamar yadda Nadabo ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), binciken farko ya nuna daukar lodin kaya da mutane da fiye da kima ce musabbabin hatsarin.

“Binciken mu ya nuna mutum 73 ne a cikin motar, 59 kuma sun samu raunuka, 4 sun mutu.”

Kabir Nadabo

Nadabo ya yi kira da babbar murya ga masu ababen hawa su gujin tukin ganganci da daukar lodi fiye da ya kamata.

“Don haka, daga yanzu duk direban da aka kama da lodin kaya da mutane, za a gurfanar da shi a gaban kotu da laifin jefa rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya cikin hatsari.

Nadabo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *