Mutum 10 sun rasa rayunkasu a hatsarin mota a jihar Jigawa

Mutum 10 sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a garin Kwanar Gujungu da ke Karamar Hukumar Taura da ke Jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya bayyana cewa motoci biyu; Golf mai lambar Auy 292 XA da dauke lamba NSR 469 AE, da suka yi da gaba-da-gaba.

Shiisu, ya ce Honda din na dauke da fasinjoji biyar, yayin da Golf din take dauke da fasinjoji hudu.

“Misalin karfe 12:00 na safe, ranar avatar wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutum 11 a garin Kwanar Gujungu, lokacin da motoci biyu suka yi karo da juna.

ASP Lawan Shiisu

“Sakamakon haka duka mutum 10 da ke cikin motocin biyu sun rasu,” in ji shi.

Ya ce tawagar ‘yan sanda daga babban Ofishinsu da ke Taura, ta garzaya zuwa wurin inda suka kai wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin, Taura, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

“Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ahmadu Abdullahi, ya aike ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *