Gwamnatin Kaduna ta ba da tallafin abinci ga kiristocin tudun biri

Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna ne ya kai kayan abinci domin taya Kiristocin murnar bikin Kirsimeti.

Aruwan ya kuma kasance cikin wadanda suka yi ibada a Cocin Nagarta Baptist da ke kauyen na Tudun Biri.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai Kiristoci yara akalla uku da suka rasa rayukansu sakamakon harin jirgin sojoji wanda ya rutsa da su a ranar 3 ga Disamba a lokacin da Musulmin garin ke gudanar bikin Maulidi.

“Mun zo ne domin taya mutanen garin Tudun Biri musamman Kiristocin garin murnar ranar Kirsimeti domin nuna musu cewa ba a mance da su ba, sannan muga cewa sun yi bikin Krsimeti lafiya cikin natsuwa”

Samuel Aruwan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *