Gwamnan Bauchi ya bukaci kiristocin Najeriya su yi wa Tinubu addu’ar samun nasara

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya bukaci mabiya addinin kirista a fadin kasar nan da su yi amfani da lokutan Kirsimeti wajen yi wa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’ar samun nasara.

Gwamnan Bauchi ya jaddada cewa “batun siyasa ya kare, lokaci ya yi da za a yi aiki, don haka yana bukatar addu’o’inmu na hadin gwiwa don samun nasara. Ku yi masa addu’a kuma ku yi mini addu’a.”

Bala Mohammed wanda ke magana a wajen wani gangamin kirsimeti da kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar ta shirya, ya ce, “Babu batun jam’iyyar siyasa a yanzu, a yi addu’a ga APC da PDP su samu nasarar yi wa al’ummar kasar aiki.”

“Idan shugaban kasa bai yi abin a zo a gani ba, hakan zai shafe mu ma a jihar. Ya kamata mu hada kai, mu tabbatar da cewa jama’a sun samu ribar dimokuradiyya.”

Ya kuma jaddada cewa addu’a na da matukar muhimmanci wajen sauya yanayi zuwa mai kyau yana mai cewa, “Allah a shirye ya ke ya amsa addu’o’inmu. Mu yi wa gwamnatin tarayya addu’ar samun karin kudi domin ci gaban jiharmu.”

Gwamnan ya tabbatar da cewa zai ci gaba da yi wa al’ummar jihar hidima inda ya jaddada cewa zai yi fiye da yadda aka yi a wa’adinsa na farko domin a cewarsa ya zo ne da niyyar yi wa al’ummar jihar aiki.

Bala Mohammed ya yabawa al’ummar kiristoci a jihar kan goyon bayan da suke ba shi da gwamnatinsa tun a shekarar 2019 da aka zabe shi a matsayin Gwamna da kuma a 2023 da aka sake zabensa a karo na biyu.

Ya kuma jaddada bukatar jama’a su rika yiwa gwamnati hisabi domin ganin an yi abin da ya dace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *