Shettima da Ganduje sun samu mukaman sarauta

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje, sun samu mukaman sarauta a jihar Anambra.

An bai wa Shettima da Ganduje sarautar gargajiya a bikin Ofala karo na 32 na Ukpo Dumukofia a ranar Asabar.

An raba hotunan bikin a shafin X na jam’iyyar APC a ranar Lahadi.

Hotunan sun yi lakabi da, “Shugaban Jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima sun samu mukaman sarauta a jihar Anambra.

“HM Igwe Dr. Robert C. Eze (Okofi VI) ne ya ba shugabannin biyu mukaman a yayin bikin Ofala na 32 na Ukpo Dumukofia a ranar Asabar.

“Yarima Arthur Eze ne ya dauki nauyin Bada mukamin Sarautar, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, IGP Kayode Egbetokun, da wasu mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) sun halarci taron.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *