CBN ya janye haramcin da ya sanya kan amfani da kudaden Crypto a Najeriya

Babban Bankin Najeriya ya janye haramcin da ya sanya kan amfani da kudaden Crypto a Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito a wata sanarwa daga Daraktan Kudade na (CBN), Haruna Mustapha, cewa an janye haramcin kan kudaden  Crypto.

Shekaru biyu ke nen bayan haramcin da CBN ya sanya wa kudaden na Crypto a watan Fabrairun shekarar 2021.

Mustapha ya bayyana cewa nan gaba CBN zai fito da ka’idoji da dokokin amfani da kudaden na Crypto domin hana wuce gona da iri wajen amfani da su a Najeriya.

A watan Fabrairun 2021 ne CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin hadahadar kudade amfani da kudaden Crypto ko bude wa masu su amfani da su asusun ajiya.

A wancan lokacin, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya sanar cewa daukar matankin na da muhimmanci domin dakile yiwuwar amfani da kudaden na Crypto wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Bugu da kari, kudaden na crypto suna tatare da hadari, sannan babu dokokin da ke kula da su ko na kare kwastomi wajen yin cinikayya da su.

Daraktan na CBN ya ce abubuwan da ke faruwa a duniya suna nuni ga muhimmanci tsara dokokin kula da kadarorin intanet irin su kudaden crypto da dangoginsu.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu ba a amince wa bankuna da cibiyoyin hadahadar kudade su mallaki kudaden Crypto ko su yi kasuwanci da su ta asusun ajiyarsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *