Ministan yada labarai: “Matsalar rashin tsaro ta bata sunan Najeriya a idon duniya”.

A ranar Juma’a ne gwamnatin Najeriya ta yi kira da a nuna kishin kasa, da kuma tallafa wa sojojin kasar domin ciyar da kasar nan gaba.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Alhaji Mohammed Idris ne ya yi wannan kiran a lokacin da babban hafsan sojin kasa Janar Christopher Musa ya kai masa ziyarar ban girma a Abuja.

A cewarsa, tashe-tashen hankula a Najeriya sun fice daga akidu zuwa fa’idar tattalin arziki.

Ministan ya bayyana hakan a matsayin abin takaici game da tashin bam a jihar Kaduna inda sojoji suka kashe ‘yan Najeriya sama da dari bisa kuskure.

Idris ya ce lokacin da muke fama da matsalar tada kayar baya da kuma ‘yan fashi, hakan ya ba wa kasar nan mummunar akida, kuma idan ba a dauki kowane irin mataki ba, to za a samu matsala.

Tunanin kishin kasa dole ne a dawo da shi a cikin zukatan yan kasar, domin mun ga yadda al’ummarmu ta lalace.

Duk da haka, yana da muhimmanci mutane su san abin da Sojoji ke yi,suna aiki dare da rana, har ma suna biya mana farashi mai yawa don samun zaman lafiyarmu tareda kasarmu baki daya.

Abin da ya faru a Tudun Biri da ke Jihar Kaduna abin takaici ne, kuma Shugaba Bola Tinubu ya ba da hakuri muna rokon cewa, a karo na gaba, a yi taka-tsantsan.

Duk da haka muna so mu gode wa rundunar sojojin saboda duk abin da suka yi kuma har yanzu suna yi don kiyaye mu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *