Mai binciken babban bankin Najeriya ta gano asusun banki 593 da Emefiele ya boye kudade a kasashen waje

Babban Mai Binciken Babban Bankin Najeriya (CBN) da Shugaba Bola Tinubu ya nada ya zargi tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele, da bude asusun ajiya guda 593 ta bayan fage a kasashen waje.

Rahoton da mai binciken ya mika wa Shugaba Tinubu ya nuna Emefiele ya yi gaban kansa ne wajen bude asusun ajiyar kasashen wajen, ba tare da amincewar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kwamitin gudanarwan CBN ba.

Takardun binciken da wakilinmu ya gani sun nuna nuna cewa Emifiele ya bude asusun ne bankuna daban-daban a kasashen Birtaniya, Amurka da kuma China.

Duk da cewa ba a bayyana sakamakon binciken a hukumance ba, amma majiya mai tushe a fadar shugaban kasa ta tabbatar wa wakilinmu cewa an mika wa Shugaba Tinubu rahoton a ranar Laraba, 20 ga watan nan na Disamba, 2023.

A ranar 9 ga watan Yunin 2023 ne Tinubu ya dakatar da Emefiele, kuma tun daga jami’an tsaro ke tsare da shi.

A ranar 30 ga watan Yuli Tinubu ya nada babban jami’in hukumar bayar da rahoton kudi ta Najeriya, Jim Obazee, a matsayin mai bincike na musamman na CBN.

A wasikar nadin, Tinubu ya bukaci Obazee ya binciki CBN da kuma manyan cibiyoyin kasuwanci na gwamnati, kuma “wannan nadin zai kasance tare da aiki nan take kuma ka mika rahoto ga ofishina kai tsaye.”

Takardun da wakilinmu ya gani a ranar Alhamis sun nuna cewa kawo yanzu rahotanni biyu aka mika wa Tinubu, kuma na karshen cikinsu shi ne na ranar 20 ga watan Disamba, da ke bayyana laifukan da ake tuhumar Emefiele da sauran su.

Rahoton ya kuma bukaci a gurfanar da wasu manyan jami’an CBN da suka yi aiki da Emefiele, da kuma wasu daga wajen CBN, bisa zargin wasu laifuka daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *