Gwamnatin tarayya ta sha alwashin kawo karshen rashin tsaro a shekarar 2024

Gwamnatin tarayya ta sha alwashin kawo karshen rashin tsaro a shekarar 2024, inda ta kara da cewa ta fahimci kalubalen tsaro da ke addabar al’ummar kasar.

Karamin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle ne ya bayyana haka a wata hira da BBC Hausa.

Matawalle ya bayyana fatansa na ganin matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na hana tashe-tashen hankula zai taimaka wajen magance hare-haren ‘yan bindiga.

“In Allah ya yarda, daga yanzu zuwa 2024, za a shawo kan duk wasu matsalolin tsaro,” in ji Matawalle yayin da yake jaddada cewa gwamnatin tarayya ta tsaya tsayin daka wajen daukar matakan yaki da ‘yan bindiga.

Ministan ya kuma jaddada cewa gwamnonin jihohin da ke fuskantar matsalar rashin tsaro suna aiki tare da gwamnatin tarayya domin shawo kan kalubalen.

Ya yi kira ga gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ya nemi hadin kan hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya, domin samun nasara a yaki da rashin tsaro.

Ya ci gaba da cewa, “Gwamnan jihar bai taba tuntubata ni da Badaru ba ko kuma ya nemi ganawa da mu kan matsalar tsaro a jiharsa.

“Don haka ina kira ga gwamnan da ya nemi hadin kan jami’an tsaro da gwamnatin tarayya domin ba zai iya yin aikin shi kadai ba.

“Kada ya damu da abin da ke tsakanina da shi, ya rika tunanin al’ummar jihar Zamfara. A ajiye duk wata siyasa a gefe, mu hada kai don nemo mafita ga jihar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *