Kotu ta tabbatar da Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa

Kotun daukaka kara ta tabbatar da Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan Adamawa.

Hukuncin Kotun daukaka kara ya zo daidai da na kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar Adamawa da ya tabbatar da zaben Fintiri.

Tun da fari yar takarar gwamnan jihar ta jam’iyyar APC, Aisha Binani ce ta daukaka kara kan hukuncin kotun.

Zaben gwamnan ya haifar da cece-kuce lokacin da kwamishinan zaben lokacin, Hudu Yunusa Ari, ya ayyana Aisha Binani ta jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe, alhali ana cikin kirga kuri’u.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *