Kotu ta yi watsi da karar da Binani ta shigar

A ranar Litinin ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC da ‘yar takarar gwamna, Sanata Aisha Dahiru Binani suka shigar na neman soke zaben Umar Ahmadu Fintiri a matsayin zababben gwamnan jihar Adamawa.

Kotun daukaka kara ta bayyana cewa kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta ayyana gwamna Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukuncin da Mai Shari’a Tunde Oyebanji Awotoye ya rubuta ya yi watsi da shari’ar Binani da APC bisa wasu dalilai na rashin gaskiya.

Daga cikin dalilan, Kotun daukaka kara ta bayyana cewa Binani da APC sun kasa kiran wakilan zabe da suka halarci zaben a matsayin shedu amma abin takaici sun kira Coordinators na yakin neman zabe wadanda ba su a wurin zaben.

Mai shari’a Awotoye ya ce shaidu ukun da aka kira a kananan hukumomi 27 wadanda suka kasance masu gudanar da yakin neman zaben shedu ne kawai wadanda ba wakilan jam’iyyar ba.

Kotun ta ce ya sabawa doka a danganta dabi’u na shari’a ga shaidar masu gudanar da yakin neman zabe tun da irin wannan ba shi da amfani a fuskar doka.

Baya ga haka, Mai Shari’a Awotoye ya ce takaitaccen gardamar da Binani da APC suka shigar ya saba wa doka, don haka bai dace ba kuma ya cancanci a yi watsi da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *