Jami’an tsaro sun kama dalibi a Jami’ar ATBU dauke da bindiga

Jami’an tsaro sun damke wani dalibi a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Jihar Bauchi dauke da bindiga da harsashi.

Dalibin dan aji 3 uku ne, kuma ’yan sanda sun cafke shi ne da bindigar  hannu ce bayan ya fito daga harabar jami’ar da ita,

Kakakin ’yan sandan jihar, Mohammed Wakil ya ce ana kama dalibin ne a lokacin da yake kokarin hada wasu gungun dalibai.

Wakil ya ce dalibin ya gaya musu cewa hayar bindigar ya karbo na shekarar karatu guda daga wurin wani.

Dalibin ya shaida musu cewa ya karbo bindigar ce domin kare kansa daga masu aikata muggan laifuka.

Jami’in ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Mohammed Musa, ya ba da umarnin gudanar da bincike domin gano ainihin dalilin dalibin na mallakar bindigar da kuma ko ya taba amfani da ita sannan a gurfanar da shi a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *