Gwamnonin arewa suna ganawar sirri, sun yi Allah-Wadai da harin hm tudun biri

Gwamnonin jihohin Arewa 19 karkashin kungiyar gwamnonin Arewa suna taro a Kaduna a halin yanzu.

Gwamnonin dai suna tattaunawa ne a kan batutuwan da suka shafi rashin tsaro, noma, da hako mai a yankin.

Sannan a Yayin Taron sun jajanta wa gwamnan mai masaukin baki game da harin da jirgin sama ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi da ke jihar inda rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin daukar alhakin Kai Harin.

Taron da Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ke shiryawa, shi ne taro na farko da gwamnonin suka yi tun bayan hawan gwamnoni kan mulki a zaben watan Mayun 2023.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, da mataimakan gwamnonin jihohin Jigawa, Bauchi, Kano, Yobe, da Kwara, wadanda ke wakiltar gwamnonin jihohinsu.

Da yake jawabi ga takwarorinsa, Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Yahaya, a lokacin da yake yin Allah wadai da harin bam da aka kai kan al’ummar Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, ya yi nuni da cewa, akwai bukatar Gwamnonin yankin su kara zage damtse wajen yaki da rashin tsaro da ke addabar al’ummar yankin.

Ya ce har yanzu magance matsalar rashin tsaro da sauran kalubale na da matukar muhimmanci ga ci gaban al’ummar yankin.

Ya kuma ba da tabbacin cewa kungiyar Gwamnonin Arewa a karkashin jagorancinsa, na aiki tukuru don ganin cewa ba a karkatar da lamarin Tudun Biri a karkashin kafet ba amma an yi bincike sosai.

Ya ce, an yi hakan ne domin tabbatar da cewa an biya wadanda abin ya shafa da kuma daukar matakin kariya don hana sake afkuwar irin wannan lamarin anan Gaba.

Ya ce, “Bari in fara da jajanta wa mutanen Tudun Biri da suka rasa rayukansu sakamakon harin bam da sojojin Najeriya suka yi ba tare da niyya ba.

“Dukkanmu mun shaida irin barnar da aka yi kuma duk mun yi tir da lamarin. Tunani da addu’o’in mu na tare da iyalai da abin ya shafa da daukacin al’ummar jihar Kaduna baki daya.

“Ina so in tabbatar muku da cewa dukkan gwamnonin Arewa suna bakin kokarinsu wajen ganin an yi bincike sosai kan lamarin da nufin biyan diyya ga wadanda abin ya shafa tare da daukar matakan gyara domin hana afkuwar lamarin nan gaba.

“A matsayinmu na gwamnonin jihohin Arewa, yayin da muke yaba wa Gwamnatin Tarayya kan yaki da rashin tsaro, mun yi imanin cewa akwai bukatar a kara kaimi wajen kawo karshen garkuwa da mutane, ‘yan fashi, rikicin kabilanci, da kuma ta’addanci da ke addabar yankinmu.”

Ya kara da cewa, “Yankinmu na fama da kalubalen rashin tsaro. Alamu na ci gaban ɗan adam yana raguwa.

“Domin kungiyar gwamnonin Arewa ta ci gaba da kasancewa masu dacewa, dole ne mu samar da hadin kai a tsakanin al’ummarmu, mu hada kai kan al’amuran ci gaba.

“Wajibi ne gwamnonin Arewa su hada kai don karfafawa jama’a a matsayin manyan rundunonin samar da ci gaban Arewa.

“Wannan yana buƙatar tsara manufofi da aiwatarwa da gangan, ta hanyoyin da suka fahimci muhimmiyar rawar da jagoranci ke takawa wajen jagorantar irin waɗannan shirye-shiryen.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *