ECOWAS ta dakatar da Nijar daga kungiyoyin yankin a hukumance

A hukumance Kungiyar ECOWAS ta dakatar da Nijar daga kungiyoyin yankin

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, ta dakatar da Jamhuriyar Nijar a hukumance daga dukkan ƙungiyoyin yankin har sai an dawo da tsarin mulkin kasar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, biyo bayan shawarar da aka yanke a taron shugabannin kasashe da na gwamnatocin da aka gudanar ranar Lahadi a Abuja.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Har zuwa zaman taro karo na 64 da aka gudanar a ranar 10 ga watan Disamba, 2023, taron shugabannin kasashe da na gwamnatocin kasar ya dauki halin da ake ciki a Nijar a matsayin yunkurin juyin mulki, inda kuma aka ci gaba da daukar Mohamed Bazoum shugaban jamhuriyar Nijar.”

“Saboda wannan matsayi, ba a dakatar da Nijar daga kungiyoyin ECOWAS masu yanke shawara ba, kuma an ba wa mambobin gwamnatin Bazoum izinin wakiltar Nijar a taron ECOWAS.”

Taron na ranar 10 ga watan Disamba ya amince cewa an hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum ta hanyar juyin mulkin da sojoji suka yi.

Sanarwar ta kara da cewa, daga ranar 10 ga watan Disamba, 2023, an dakatar da Nijar daga dukkan hukumomin da suka yanke shawara na ECOWAS, har sai an maido da tsarin mulki a kasar.

Taron shugabannin kungiyar ECOWAS a Abuja a ranar Lahadi ya bukaci gwamnatin mulkin sojan Nijar da ta hau karagar mulki a ranar 26 ga watan Yuli, da ta saki hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum domin a dage takunkumin da aka kakabawa kasar.

Sai dai shugaban gwamnatin mulkin soji Omar Abdourahmane Tchiani ya yi watsi da shawarar, inda ya sake jaddada cewa ba za a saki Bazoum ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *