Hukumar karota ta cafke mota da ta dauko giya kwalba 4,600.

Shugaban Hukumar KAROTA, Faisal Mahmud Kabir ne ya sanar da hakan a lokacin da yake sanar da cewa hukumar bankado wani sabon salon da direbobi suka kirkira wajen shigo da giya jihar

Jami’an da suka cafke motar sun bayyana cewa a lokacin da suka tsayar da motar, direban ya shaida musu cewa itacen girki ya dauko.

Amma bayan da aka matsa da bincike sai aka fahimci ba itacen ba ne, barasa ce a ciki.

Shugaba Hukumar ya ce da zarar an kammala bincike za a mika giyar ga Hukumar Hisbah domin fadada bincike da daukar mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *