CBN ya dakatar da biyan kudaden da ake kashewa a kan wasu makudan kudade sakamakon karancin naira

Mukaddashin Daraktan Sa ido na CBN, Dr Adetona Adedeji, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.

Sabon ci gaban a ƙarƙashin “Jagorar cajin Bankuna, Sauran Cibiyoyin Kuɗi, da Cibiyoyin Kuɗi da ba na Bankunan ba” da aka bayar a ranar 20 ga watan Disambar shekarar 2019, tare da lamba (FPR/DIR/GEN/CIR/07/042), yana shafar ajiyar kudi na sama da Naira dubu N500,000 na asusun mutum daya da Naira Dudu N3,000,000 na asusun kamfani.

Babban bankin ya ce dakatarwar za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 30 ga watan Afrilu, 2024.

Babban bankin na CBN ya kuma bayyana cewa a asusun kamfanoni, bankunan ajiya za su rika karbar kudaden sarrafawa kashi biyar bisa dari na kudaden da za a cire da kuma kashi uku bisa dari na kudaden da aka ajiye a sama da Naira dubu N3,000,000.

“Saboda haka, duk cibiyoyin hada-hadar kudi da CBN ke kula da su ya kamata su karbi duk kudaden ajiye daga hannun jama’a ba tare da an karbi kudade a wajen su ba,” in ji CBN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *