“Ba zan gamsu ba har sai an kawo karshen rashin tsaro gaba daya a Najeriya”.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana a ranar Litinin cewa ba zai gamsu ba har sai an kawo karshen rashin tsaro gaba daya a Najeriya.

Tinubu yayi magana ne a ziyarar da ya kai fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi.

Ya ce yaki da rashin tsaro yana da kyau tun bayan hawan gwamnatinsa.

Tinubu ya yi alkawarin cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen bayar da tallafi da kulawa ga iyalan dukkan ‘yan Nijeriya da suka yi fama da matsalar rashin tsaro a sassan jihar Borno.

A cewar Tinubu: “Wannan shi ne alhakina mafi tsarki kuma yanayin babban kokarin da aka nuna a sakamakon nasarar da aka samu a kan shan kaye yana zamewa da kyau tun lokacin da sabuwar gwamnati ta koma ofis.

“Har yanzu ba mu gamsu ba. Ba mu gamsu ba har sai mun kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *