Sanatoci Najeriya 109 sun bayar da gudunmawar albashin watan Disamba ga wadanda harin bam da ya rutsa da su a Kaduna.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ne ya sanar da hakan a ranar Lahadin da ta gabata a gidan gwamnatin Jihar Kaduna a lokacin da ya jagoranci wata babbar tawaga ta ‘yan majalisar dattijai zuwa jihar.

Barau ya bayyana cewar saboda matukar nuna alhini da sanatocin Nijeriya suka yi sun dauki matakin yafe dukkan albashinsu na watan Disamba,domin a tallafawa mutanen da harin bam na Tudun Biri ya rutsa dasu.

Gwamna Uba Sani ne ya tarbi Sanatocin a gidan gwamnatin jahar Kaduna an Sir Kashim House dake birnin Kaduna,inda ya nuna matukar godiyar gwamnatin jahar akan nuna kulawa da sanatocin suka yi ga wadanda harin jirgin Tudun Biri ya rutsa dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *