“Dole ne shugabannin yankin Afrika su fara lalubo hanyoyin samar da shugabanci na gari”.

Shugaban Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, Hukumar Shugabannin Kasa da Gwamnati, Bola Tinubu, ya ce dole ne shugabannin yankin su fara lalubo hanyoyin samar da shugabanci na gari.

Ya ce irin wannan fifikon zai tabbatar da samun wadata tare kuma da yiwuwar hana kwace mulki da sauye-sauyen gwamnati da ba su dace ba a yankin.

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 64 a Abuja ranar Lahadi.

A cewarsa, gudanar da mulki nagari zai zama ginshikin samun goyon bayan jama’a ta hanyar sauye-sauyen zamantakewa da tattalin arziki da ci gaban Afirka ta Yamma.

Ya ce, samar da shugabanci nagari, hanya ce da za ta magance matsalolin da ‘yan kasa ke da su, da taimakawa wajen inganta rayuwarsu, kuma zai taimaka matuka wajen samar da ingantaccen yanayi da zai kai ga samun ci gaba mai dorewa.

Tinubu ya kuma bayyana cewa, shugabanci nagari zai magance kalubalen talauci, rashin daidaito da sauran matsalolin da ke damun al’umma, yana mai jaddada cewa, da shugabannin Afirka za su yi nasarar magance wasu daga cikin dalilan da suka haifar da tsoma bakin sojoji a harkokin farar hula a yankinmu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *