Kwamishinan ‘yan sandan Gombe ya gabatar da tallafin kudi N80m ga iyalan jami’an da suka rasu

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe, CP Hayatu Usman, wanda ya wakilci babban sufeton ‘yan sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya gabatar da chekin kudi sama da naira miliyan 80 ga iyalai 19 na ‘yan sandan da suka rasu a jihar.

An gudanar da wannan aikin na alheri ne a ƙarƙashin ikon IGP Welfare Family and Group Assurance Plan.

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Kakakin ‘yan Sandan Jihar Gombe ASP Mahid Muazu ya fitar ranar Juma’a Wanda aka ta tabbatar ta shafinsu na X @GombePoliceNG. yace Bikin ya gudana ne a hedikwatar rundunar da ke Gombe.

Bikin ya shaida taron dangi na kusa da ‘yan sandan da suka rasa rayukansu a bakin aiki a fadin kasar.

Usman, a madadin rundunar ‘yan sandan, ya nanata jajircewarsa ga iyalan jami’an da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare lafiya da rayuwar al’umma.

Kwamishinan’yan Sandan Hayatu Usman ya ja hankalin wadanda suka amfana da su yi amfani da kudaden cikin adalci wajen biyan bukatun iyalansu, inda ya jajanta musu tare da ba su tabbacin taimakon rundunar ‘yan sanda.

Ya kuma dauki lokaci mai tsawo yana gabatar da addu’o’i ga rayukan jami’an da suka rasu, yana mai yi musu fatan zaman lafiya.

A nasa martani, wakilin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ya nuna matukar godiya a madadin iyalai, inda ya yaba wa shugabannin ‘yan sandan Najeriya bisa yadda suka tausaya musu, tare da amincewa da rage musu nauyin kudi Wajen biyan bukatun zawarawa da yara, da sauran wadanda jami’an da suka rasu suka bari a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *