Gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 178 daga cibiyoyin gidan gyaran hali da ke Jigawa

Gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 178 daga cibiyoyin gidan gyaran hali da tarbiyya da ke jihar Jigawa ta hannun ma’aikatar harkokin cikin gida.

Kakakin Hukumar Kula da gidan yari na Najeriya a Jigawa, Muhammad Sani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa Konturola na NCoS a Jigawa, Mista Muazu Garba-Charanchi, ya saki fursunonin a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo.

“A kokarinta na rage cunkoso a gidajen yari a fadin kasar nan, ma’aikatar harkokin cikin gida ta tarayya, tare da hadin gwiwar masu hannu da shuni da kungiyoyi, sun samu nasarar sakin fursunoni 178 a Jigawa.

“Fara atisayen a Cibiyar Kula da gidan gyaran hali da tarbiyya da ke Hadejia,Garba-Charanchi, ya yaba da kokarin ministan.

“Ya kuma yabawa masu bayar da tallafi da kuma babban jami’in gyare-gyare, Mista Haliru Nababa, bisa wannan abin yabo da kyautatawa,” in ji Sani.

Ya kara da cewa Garba-Charanchi ya koka kan yadda cunkoso a cibiyoyin gidan gyaran hali da tarbiyya da ke Jigawa ya kawo cikas ga kokarin hukumar ta NCoS a shirye-shiryen yin gyara.

Ya kuma bayyana cewa, Garba-Charanchi ya bukaci fursunonin da aka sako da su kasance masu halin kirki kuma su kasance jakadu nagari na zaman lafiya da tsaro.

Garba-Charanchi ya shawarci sauran fursunonin da Ake Tsare da su, da su natsu da zaman lafiya don sauwaka musu gyara da kuma jin dadin gwamnati, in ji Sani.

Ya bayyana cewa an saki fursunoni 60 daga cibiyar gidan gyaran hali da ke Hadejia daku Fursunoni 23 da ke Gumel.

An sako fursunoni 22 daga cibiyar gidan gyaran hali da tarbiyya ta Birnin-Kudu; 16 daga Cibiyar Kula da tarbiyya dake Babura; da 13 daga Cibiyar Kula da tarbiyya da ke Dutse.

An sako fursunonin takwas daga gidan yarin Kazaure; takwas daga gidan yarin Ringim; bakwai daga Cibiyar Kula da gidan gyaran hali da tarbiyya dake Jahun; da shida daga Cibiyar Kula da tarbiyya dake Kiyawa.

Sani ya ce an saki fursunoni shida daga gidan yarin Birnin-Kudu, biyar daga gidan yarin Gwaram, da hudu daga gidan yarin Garki.

Wani fursuna da aka saki wanda ya mayar da martani a madadin wadanda suka ci gajiyar, Mista Umar Sanda, ya gode wa gwamnatin tarayya da hukumar NCoS bisa Ganin su a matsayin wadanda suk dace a biya su tarar da aka biya duk da laifukan da suka aikata.

Ya kuma nuna jin dadinsa da yadda gwamnati da abokan huldarta suka baiwa fursunonin da aka sako wasu alawus.

Sanda ya ba da tabbacin cewa fursunonin da aka sako za su sanya basirar da aka samu a cibiyoyin gidan gyaran hali da tarbiyya don yin aiki don dogaro da kai da kuma guje wa aikata laifuka anan gaba.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, an biya wa fursunonin da aka sako kudaden alawus-alawus, don taimaka musu wajen komawa gidajensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *