Kotu ta umurci Matawalle Ya mayar da motocin gwamnati 50 da ke hannunsa

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Sokoto ta umarci tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da ya mayar da dukkan motocin Gwamnati da ke hannun sa.

Rahma ta tuna cewa a watan Yunin 2023 ne gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da wa’adin kwanaki biyar ga tsohon gwamnan da mataimakinsa da su dawo da duk motocin da aka ce sun tafi da su.

Bayan da Matawalle ya ki mayar da motocin guda 50, gwamnatin jihar ta bi umarnin kotu na karbo kadarorin.

Bayan haka, an kwato motoci sama da 50 daga hannun tsohon gwamnan bisa kokarin rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Sai dai bayan an kwato motocin, Matawalle ya kai karar zuwa babbar kotun tarayya da ke Gusau.

Daga nan ne kotun ta bayar da umarnin a mayar masa da motocin.

Hakazalika tsohon gwamnan ya shigar da wata kara ta daban a wannan kotun, inda ya nemi ta tabbatar masa da hakkinsa na mallakar kadarori, ciki har da motocin da ake magana a kai.

Sai dai gwamnatin jihar ta bukaci a mayar da shari’ar zuwa wani hurumin babban kotun tarayya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Litinin, ya ce babbar kotun tarayya da ke zamanta a Sokoto ta yi watsi da batun a ranar Juma’a tare da bayar da umarnin a mayar da motocin ga gwamnati.

“Kotu ta ki amincewa da tallafin da Bello Matawalle ya nema, ta kuma yi watsi da ikirarin nasa na mallakar motocin Gwamnatin.

“Saboda haka har yanzu motocin ana daukar su mallakin gwamnatin jihar Zamfara.

“Gwamnatinmu ta kuduri aniyar kwato duk wani abin da ya dace na jama’a ta hanyar aikin ceto da ba zai bar kowa ba.

“Hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, zai kara mana kwarin gwiwar tabbatar da cewa an hukunta duk wanda ya aikata laifin ta’addanci a Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *