Hukumar Kwastam ta shiyyar Kano ta samar da naira biliyan N6.9 cikin wata 1

Hukumar Kwastam ta shiyyar Kano ta ce ta samu Naira biliyan 6.9 a matsayin kudaden shiga a watan Nuwamba, kamar yadda Kwanturolan hukumar Mista Dauda Ibrahim Chana ya bayyana a ranar Litinin.

Chana, wanda ke kula da shiyyar jihar Kano da Jigawa, ya kuma bayyana cewa, “Mun kuma kama buhunan shinkafa ‘yar kasar waje buhu 2,817, tayoyin da aka yi amfani da su guda 1,428, jarkokin man abinci guda 250 mai lita 25 da kuma katandin sabulu 690 na kasar waje.

“Sauran kayayyakin da aka kama sun hada da bales guda 429 na kayan sawa na hannu, fakitin Royal tramadol guda 1,226, sinkin tabar wiwi guda 470 da katan 1,530 na spaghetti na kasashen waje.

Kwanturolan ya ce rundunar ta bullo da wasu tsauraran matakan tsaro domin dakile duk wani nau’in fasa kwauri a yankin.

“Mun riga mun sanya jami’an mu a wurare masu mahimmanci don magance duk masu hannu a cikin haramtattun safarar kayayyakin.”

Ya ce rundunar hukumar ta yankin ta bayar da umarnin tura jami’anta zuwa kan iyaka da ke Maigatari a karamar hukumar Gumel a jihar Jigawa domin kara kaimi wajen dakile ayyukan masu fasa kwauri.

“An kuma aike da wannan umarni ga jami’an da ke ofishin Jeke da ke karamar hukumar Babura a jihar Jigawa.

Kwanturolan ya ce “A shirye muke mu kawo karshen fasa-kwaurin ta hanyar dabarun mu daban-daban, domin share fagen kamawa da gurfanar da masu fasa-kwauri.”

Chana ya nemi goyon bayan sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan mazauna yankin kan illar fasa-kwauri ga tattalin arzikin kasa.

“Mun kuma tuntubi matasa a yankunan kan iyaka da su taimaka wa jami’an mu da bayanan sirri da ake bukata wadanda za su taimaka wajen dakile duk wani nau’in safarar mutane.

“Yankin da rundunar ta ke da shi wuri ne na masu fasa-kwauri, domin an tanadi jami’an da suka kware wajen gano hanyoyin fasa kwabri domin tabbatar da kamawa da gurfanar da masu laifi.”

Ya kuma nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan jama’a domin su guji fasa-kwauri da rungumar fitar da kayayyakin cikin gida zuwa kasashen waje. NAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *