“Ilimi ba zai bunkasa ba sai da tsaro” – Dikko Radda

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ce ilimi ba zai bunkasa ba sai da tsaro.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wajen taron hadaka na yaye dalibai karo na 7 da na 8 na Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, ranar Asabar.

Radda ya jaddada muhimmiyar alakar tsaro da ilimi mai ma’ana, yana mai cewa babu shakka, “Ba za a iya samun ilimi mai ma’ana ba sai da tsaro.”

Ya nuna matukar damuwarsa kan tasirin ‘yan fashi a makarantu, lamarin da ya haifar da cikas da rufewa, tare da dakile damar karatun dalibai.

Dangane da wadannan kalubale, Radda ya lura cewa, gwamnatinsa ta aiwatar da dabarun karfafa tsaro a makarantu.

A cewarsa, Bisa Hakan an kafa kungiyar sa ido ta al’ummar jihar Katsina da nufin tabbatar da tsaro a cibiyoyin ilimi a fadin jihar.

Radda ya ce, “Babu ilimi ba tare da tsaro ba. Da yawa daga cikin kananan hukumomin mu na gaba an rufe makarantunsu saboda ‘yan fashi, wasu lokutan kuma makarantu sun zama kogon ‘yan fashi.

”Wannan ne ya sa muka kafa kungiyar sa ido ta jihar Katsina domin yaki da rashin tsaro da samar da wata gidauniya ta yadda matasanmu za su iya koyo da ci gaba.

“Lokacin da muka ce abin da muka fi mayar da hankali a kai shi ne gina makomar al’ummarmu, shi ne muke nufi, duk ayyukan da muka fara a matsayin gwamnati an tsara su ne domin shimfida ginshikin samun kyakkyawar makoma ga al’ummar Katsina.

Dangane da batun yaran da ba sa zuwa makaranta, Radda ya bayyana shirye-shiryen sake shigar da su cikin ilimin boko ta hanyar hada kai da abokan hadin gwiwa da cibiyoyin addini don samar da muhimman kayan aikin ilimi da samar da hadin kai a cikin tsarin ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *