Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sake tabbatar wa Uba Sani Kujerar Gwamnan Kaduna

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja a ranar Juma’a ta tabbatar wa Uba Sani kujerarsa a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna.

Kotun mai alkalai uku cikin murya daya dai ta yi fatali ne da karar dan takarar PDP a zaben da ya gabata, Isah Mohammed Ashiru, saboda ta ce ba ta da hujja.

Ashiru dai ya garzaya kotun ne yana kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wacce ta tabbatar wa da Uba Sani nasara a zaben, kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana.

A cewar INEC a wancan lokacin, Uba ya lashe zaben ne da kuri’a 730,002, inda ya doke Isah mai kuri’a 719,196.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *