Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta gargadi fasinjoji da su guji yin tafiye-tafiye cikin dare

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta gargadi fasinjoji da su guji yin tafiye-tafiye cikin daddare a lokacin bukukuwan kirsimeti saboda illar da za su iya fuskanta.

Mista Ibrahim Maiyaki-Bazama, Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar Katsina ne ya yi wannan gargadin yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Katsina.

“Mutane suna da ‘yancin yin tafiya, amma mu a matsayinmu na jami’an kiyaye hadurra, muna da hurumin daukar matakan da za su taimaka wajen rage hadurran hanyoyi.

“Wani bangare na irin waɗannan matakan shine mu ƙarfafa mutane su daina ko rage tafiye-tafiyen Cikin dare.

“Wannan shi ne saboda idan direban mota ke tuƙi da daddare, ba ya iya gani sama da iyawar hasken fitilar motar.

“Idan wani hatsari ya faru, wani lokacin ba sa samun masu taimako ko kuma yana ɗaukar lokaci kafin a sami waɗanda za su taimaka,” in ji shi.

Maiyaki-Bazama ya kuma bayyana cewa, rundunar tana da tawagogin masu aikin ceto a shirye suke su tafi idan lamarin gaggawa ya faru.

Ya bayyana cewa, tawagar sun kasance a runfunan runduna biyar na Funtua, Daura, Koza, Malumfashi da kuma Kankia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *