Tinubu ya amince da nadin sabon Kwamishinan hukumar raba dai-dai

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Ambasada Desmond Akawor a matsayin kwamishinan gwamnatin tarayya na hukumar tattara kudaden shiga da rabon kudi da kasafin kudi (RMAFC), har sai majalisar dattawan Najeriya ta ida tabbatar da shi.

Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa ya amince da nadin sabon kwamishinan tarayya na RMAFC mai wakiltar jihar Rivers ne biyo bayan rasuwar tsohon kwamishinan jihar, Hon. Asondu Wenah Temple, farkon wannan watan.

Akawor ya yi wa kasa hidima a matsayin Jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu; Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT); Shugaban Karamar Hukumar Raya Fatakwal; Shugaba, Hukumar Raya Kogin Neja Delta, kuma Babban Darakta, Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (Engineering & Technical Services).

Shugaban ya umarci sabon kwamishinan da ya ba da kwarin gwiwar kwarewarsa a cikin matakan gwamnati don inganta ingantaccen tsarin da zai tabbatar da mafi inganci da amfani da kasafi ga dukkan matakai uku na gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *